DA DUMI-DUMI: Osagie Ize – Iyamu ne ya lashe zaben fidda gwanni a Edo

Osagie Ize – Iyamu ya lashe zaben neman tikitin takarar kujerar gwamnan jahar Edo a karkashin inuwar jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a yau Litinin, 22 ga watan Yuni 2020.
Gwamnan jahar Imo, wanda shine shugaban kwamitin zaben fidda gwanni  a jahar, Hope Uzodinma ne ya bayyana hakan a birinin Benin City.

Ize-Iyamu ya samu nasarar lashe zaben na fidda gwani  ne da Kuri’u 27,838 wanda hakkan ne yasa ya duke abokin takarar sa Pius Odubu wanda ya samu kuri’u 3,776 sai kuma Osaro Obaze ya samu 2,724.

Hakkan ne zai bawa Ize-Iyamu damar karawa a zaben mai zuwa 19 ga watan satumba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More