DA DUMI- DUMI: Sarkin Zazzau ya rasu da shekaru 84 a Duniya

Allah ya yiwa sarki Zazzau Shehu Idris,   rasuwa a yau Lahadi 20 ga watan Satamba 2020.

Sarki Idris ya rasu yana da shekaru 84 a Duniya,  rahotunni sun nuna cewa, ya rasu ne a  asibitin  44 na sojoji dake jahar Kaduna bayan fama da gajeruwar  rashin lafiya.

Sarki Idris ya  shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Za a yi jana’izar sa da misalin karfe  5 na yammacin yau Lahadi, kamar yadda Gwamnan jahar Kaduna, Nasiru Elrufa’i ya fitar da sanarwar a shafinsa na Twitter, bayan yayi ta’aziyyar rasuwar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More