DA DUMI-DUMI: Shoprite ta fara shirin janyewa daga Najeriya

Katafaren kantin nan na sayar da kayayyaki Shoprite,  zai daina gudanar da harkokin kasuwancinsa a Najeriya bayan shekaru 15 da budewa.

Shoprite ta fitar da sanarwar hakkan ne a yau Litinin 3 ga watan Agusta 2020 da safe, inda ta ce masu kantin sun dauki matakin janyewa daga Najeriya ne saboda an samu mutanen da suka nuna sha’awar sayensa.

Shoprite ya bayyana Najeriya a rukunin kasashen da “za a daina gudanar da harkoki” a yayin da ya sanar da raguwar kashi 5.9 cikin dari na kasuwarsa a kasar a 2019 da kuma kashi 6.4 daga watan Janairu zuwa Yuni na 2020 saboda annobar cutar Coronavirus.

An fara bude kantin na Shoprite  ne a jahar legas a watan Disamba shekarar 2005.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More