DA DUMI-DUMI : Shugaba Buhari ya fara fitar da sunayen sabbin ministocinsa

Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya fara wallafa sunayen a sahafinsa na Twitter a yau Talata 23 ga watan Yuli 2019.
 
Daga cikin sunayen da aka fitar zuwa yanzu sun hada da Sheikh Isa Ali Pantami da Sanata Godswill Akpabio da Alhaji Sabo Nanono da Bashir Magashi daga Kano.
 
Sauran sun hada da Babatunde Fashola, Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Adamu Adamu daga Bauchi da Sanata Chris Ngige daga Anambra.
 
Akwai kuma Rauf Aregbesola tsohon gwamnan Osun da George Akume daga Benue,Timipre Sylva na Bayelsa da Adeniyi Adebayo daga Ekiti.
 
Daga jihar Oyo akwai Sunday Dare sai Festus Keyamo daga Delta,Sharon Ikeazor daga Anambra, Sanata Tayo Alasoadura daga Ondo da Olorunnibe Mamora daga Lagos, Sadiya Farouk daga Zamfara.
 
Daga Katsina shugaban ya mayar da Hadi Sirika da Zainab Ahmad daga Kaduna da Maryam Katagum ita ma daga Bauchi.
 
Akwai Lai Mohammed da Gbemi Saraki daga Kwara.
 
Tuni dai shugaban kasar ya aike sunayen ga majalisar dattijai domin tantancewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More