DA DUMI – DUMI: Shugaban ma’aikatan jahar Borno, Babagana Wakil ya rasu.

Marigayi   Dakta Babagana Wakil yayi aiki a matsayin shugaban ma’aikatar jahar na shekara daya kafin rasuwar tasa.

Mai magana da yawun gwamna Zulum,Isa Gusau ne ya fitar da sanarwar hakkan a yau 1 ga watan Yuli 2020.

Inda ya kara da cewa za’a yi janaizar marigayi Babagana gidan su na gado dake unguwar Shehuri, a arewacin birnin ma Maidugiri.

Sai dai babu wani bayani dake nuna abunda yayi sanadiyya rasuwar tasa.
Allah ya kai rahama kabarin sa. Ameen

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More