DA DUMI- DUMI: Tsohon gwamna Uduaghan ya sauya daga APC shaka zuwa PDP

 Tsohon gwamnan jahar Delta Dakta Emmanuel Uduaghan ya sauya shaka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Ana sa ran tsohon gwamnan zai ja wasu tawagar magoya bayan sa  na  mazabarsa, Abigborodo  raka’a 6  dake karamar hukumar Warri ta Arewa zuwa jam’iyyar PDP  a jahar.

Rahotunnin sun nuna cewa,Uduaghan ya gama shriye- shiryen sa na komawa  jam’iyyar PDP, wanda  a karkashin jam’iyyar ya lashe zaben sa, kuma ya dauki  shekaru takwas yana mulkar jahar ta Delta a matsayin gwamna.

Wasu daga cikin magoyan bayan tsohon gwamna Uduaghan, kuma masu yi masa biyayya, wanda saka  hada da, tsohon dan majalisar dokoki ta jahar Delta,Godwin Abigar ya sauya sheka zuwa PDP a makon da ya gabata.

Daga karshe dai  ga abunda Uduaghan yace

“Na dawo dan na hade da sojojin jam’iyyar da wasu don karfafa  jam’iyyar mu ta  PDP, wanda itace mafi girma a Afurka”. A cewar Emmanuel Uduaghan kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Litinin  26 ga watan Satamba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More