DA DUMI DUMI: Tsohon Shugaban Gidan Rediyon Kano Ya Rasu

Allah ya yiwa Umar Sa’idu Tudunwada,shugaban gidan rediyon Jahar Kano, rasuwa ba da jimawa ba a yau 30 ga watan Yuni 2019.

Ya rasu ne sakamakon hatsari mota a hanyar Garin Kura yayin da yake kan hanyar shiga cikin garin Kano bayan ya baro babban birnin tarayyar Abuja.

Mai rukon kuryar mukamin shugabancin gidan Telabijin na ARTV Kano Muhammad Sanusi Jibrin ya bayyana wa OakTV jimamin sa bisa rashi babba da yan jarida suka yi na rasuwar Umar TunduWada bayan ya dawo daga wurin janaisar sa.

Muhammad Sanusi yace Umar mutun ne mai kirki wanda dole ayi alhinin rasuwarsa domin ya bada guduma sasai wajen ganin ya koyar da dukkan wani na kasa dashi ta bagaren aiki jarida bada wani kyashi ba

A karshe yai masa fatan Aljanna Firdausi tara da fatan Allah ya kyatata dukkan makwacin musulmin inda tashi ta riske shi, tare da yiwa iyalan marigayi Umar fatan Allah ya albarkace su ya kuma basu hakurin jure rashinsa.

Marigayin ya rike kujerar mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai ga tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2011, sannan tsohon ma’aikacin sashen Hausa na VOA

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More