DA DUMI-DUMI: Yadda hukumar DSS ta sake damke Sowore

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta sake kama ma wallafin jaridar Sahara Reporters wato Omoyele Sowore kwana 1 bayan ta sake shi.

Jami’an DSS sun kama Mista Sowore ne bayan da ya bayyana a gaban kotu a Abuja don ci gaba da sauraren kararsa a yau Juma’a 6 ga watan Disamba 2019.

Jami’an sun yi yunkurin  kama Sowore tun a cikin kotun, amma sai yayi gardama, sai da lauyan  sa ya fitar dashi, sannan suka samu damar kama shi a wajen kotun.

An tafi da Mista Sowore a cikin motar lauyansa, Femi Falana SAN inda jami’in DSS ke tuka motar kuma lauyan nasa ya yi masa rakiya.

Rahotanni sun nuna cewa  ganin hukamar DSS din da bindigu ya tsorata alkaliyar, inda yasa ta  ari ta Kare  daga harabar kotun.

Tun da farko babbar kotun dake birnin tarayya Abuja ta baiwa hukumar tsaro ta DSS umarnin yin hakan ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa’a 24 tare da biyansa diyyar naira ₦100,000.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta ce umarnin sakinsa ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

Kotu ta  dage zaman sauraron karar  zuwa 11 ga watan Fabrairun 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More