DA DUMI DUMI: Yan bindiga sun kashe Shugaban PDP na Delta

Ana zargin yan bindiga da kashe Shugaban jam’iyyar PDP a Ward 4 (Olomu Ward 1) da ke yankin Ughelli ta Kudu a jahar Delta wato Mista Paul Onomuakpokpo.
Rahotannin sun kawo cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Laraba 8 ga watan Janairu 2020, a kan hanyar Ogoni kusa da fadar Ohworode na masarautar Olomu.

Nan take dai mista Paul ya rasu sakamakon alburusai da yan bindigar suka sakan masa da dama, motarsa mai kirar Toyota Camry duk ta kasance dauke da harbin bindiga.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan na ta harbi ba kakkautawa a sama, sai da suka tabbatar marigayin ya mutu kafin suka bar wajen.

A halin yanzu dai rundunar yan sandan jahar Delta ta tabbatar da lamarin yayin da kwamishinan yan sandan jahar Mista Hafiz Inuwa, ya tabbatar da afkuwar al’amarin, inda ya bayyana cewar gawar yanzu tana mortuary wata wajen ajiyar gawawwaki kuma sun shiga bincike akan lamarin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More