DA DUMI-DUMI : Yan majalisu 9 sun janye kansu yayin da ake yunkurin tsige mataimakin gwamnan jahar Ondo Ajayi

Bayan tattaunawar da yan  Majalisun jahar  ta Ondo suka yi a zauren majalisar bisa zargin saba wa dokokin aiki da ake yiwa maitaimakin  gwamnan wato Mista Agboola Ajayi, majalisar ta  cimma matsayar aike wa mataimkin gwamnan takardar  tsige shi daga mukaminsa.

Jami’an ‘yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC sun mamaye harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

Inda aka  hana ‘yan jarida shiga harabar majalisar, tare da cewa, yan jaridar su kira shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar, Gbenga Omole,  ya basu izini kafin a bari su shiga kamar yadda The Cable ta ruwaito.

‘Yan majalisa ne kawai da ma’aikatan majalisar suka samu damar shiga harabar majalisar.

Sai dai kuma zuwa yanzu yan majalisu guda tara ne suka  janye kansu daga yukurin na tsige mataimakin gwamnan  jahar ta Ondo ta hanyar rubuta wasika zuwa ga shugaban majalisa ta jahar, Honourable Bamidele David Oleyelogun.

Ga sunayen yan majalisun da suka jaye kansu:

 I. Hon Inju Ogandeji

2.Hon. Jamiu Sulaiman Maitd

3. Hon Rasheed Olalekan Elegbeleyg

4 Hon. Tomide Leonard

5.Hon. Samuel Edamisan Ades

6 Hon. Favour Semilore Tomomew

7 Hon. Festas O. Akingbasn

8 Hon Adewale Williams Adwle

9.Hon (Barr.) Torhuloto Suocss

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More