
DA DUMI-DUMI: ‘Yan sanda sun ceto wata lauya da yan bindiga suka yi awun gaba da ita a Port- Harcourt
Yan sanda sun samu nasarar ceto wata lauya mai suna Bisola Paulette Ajayi wacce masu satar mutane suka yi awun gaba da ita a makon da ya gabata.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, mai magana da yawun ‘yan sandan na jahar Rivers Nnamdi Omoni ne ya tabbatar da hakan.
Yan bindigar sunyi awun gaba ne da Paulette mai shekaru 25 a gidan ta dake Rumuokurusi a Port- Harcourt.
Lamarin ya faru ne daga karfe 8:30 zuwa karfe 9 na daren ranar Asabar, kamar yadda wani daga cikin dangin ta ya fada.