DA DUMI-DUMI: #ZabenEdo2020: Kurunkus anyi ta kare Obaseki na jam’iyyar PDP ya samu nasara lashe zaben gwamnan Jahar Edo

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta tabbatar da Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan  jahar Edo wanda aka gudanar a jiya Asabar, 2020 a karo na biyu.

Obaseki  na jam’iyyar PDP ya samu nasarar lashe zaben ne bayan  ya doke abokin hamayarsa  na Jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu ne da mafi yawan kuri’u.

Hukumar ta INEC ta bayyana  cewa, Mista Obaseki ya samu kuri’u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu kuri’u 223,619.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More