DA DUMI – DUMI: #ZabenOndo2020: Akeredolu na jam’iyyar APC ya sake lashe zaben gwamnan Jahar Ondo a karo na biyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta tabbatar da Arakurin Oluwarotimi Akeredolu na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar Ondo wanda aka gudanar a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba 2020 a karo na biyu.
Akeredolu na jam’iyyar APC ya samu nasarar lashe zaben ne bayan ya doke abokin hamayarsa, Eyitayo Jegede na jam’iyyar PDP ne da mafi yawan kuri’u.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa, gwamna Arakurin Oluwarotimi Akeredolu ya samu kuri’u 292,830 inda kuma Mista Eyitayo Jegede ya samu kuri’u 195,719.
#OakTV #OakTVHausa
#OakTVOnline