DA DUMI-DUMI: Zailani ne sabon kakakin majalisar jahar Kaduna yanzu

An rantsar da mataimakin tsohon kakakin majalisar jahar Kaduna  a matsayin sabon kakakin majalisar

Awanni kadan da suka wuce bayan honarabul Aminu Shagali ya yi murabus, Yusuf Ibrahim Zailani, ya zama  sabon kakakin majalisar jahar Kaduna.

Zailani shine mataimakin  tsohon kakakin majalisar Jahar kaduna a baya, rahotonni sun tabbatar da cewa, yan majalisun na jahar  Kaduna guda 25 ne ake zargin suka kada kurinsu na tumbuke Shagali.

An zabi Muktar Isa Hazo a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Sannan kuma an rantsar da Yusuf Ibrahim Zailani a  matsayin sabon kakakin majakisar a yau 25 ga watan Fabrairu 2020, wanda akawun majalisa jahar, barasta  Bello Zabairu ya rantsar dashi.

Sai dai wasu daga cikin yan majalisun basu gamsu da abunda ke faruwa ba, inda suke ta musayar yawu gama da lamarin, kuma an hange su a kan hanyar zuwa ofishin gwamnan jahar ta Kaduna.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More