DA DUMI- DUMI:Coronavirus ta kashe Kwamishanan lafiya na jahar Ondo Wahab Adegbenro

Kwamishanan lafiya na jahar Ondo, Dakta Wahab Adegbenro, ya rasu.

Rahotanni daga fadar gwamnatin jahar  na nuna cewa, kwamishanan ya rasu ne a asibitin da ake kula da masu Coronavirus, kuma cutar ta Covid19 ce tayi sanadiyyar mutuwar sa.

Marigayi  Wahab Adegbenro ya rasu da safiyar yau Alhamis 2 ga watan Yuli 2020, a wajen da yake kabar  magani a asibiti.

Babban mai taimaka wa Gwamna jahar ta Ondo kan ayyuka na musammam,  Odebowale Oladoyin, ya tabbatar da mutarwar ta marigayi Wahab.Sai dai  baiyi karin bayani akan abunda yayi sanadiyya mutuwarsa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More