Da kaina zan tare hanyar shiga Kaduna daga Kano naga mutumin da zai shigo mana jaha- Gwamna El-rufa’i

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-rufa’i ya ce zai tabbatar babu mutumin da zai shiga Kaduna ranar Sallah kasancewar gwamnatin jahar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma’a.

Gwamna El-rufa’i  ya bayyana hakkan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga yan jahar sa, a yau Talata 18 ga watan Mayu 2020. “Ni da kaina zan je hanyar shigo wa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. Cuta ta riga ta yi katutu a tsakanin mutane mu kuma mu bari su shigo mana da ita. Ba zai yiwu ba.” inji Gwamna El-rufa’i
Hakka kuma gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ‘cin amana’ inda ya ce jami’an tsaro na karbar na goro domin barin jama’a su shiga jahar ta Kaduna.  Gwamna Elrufa’i ya ce kowa ya yi sallar idi da Juma’a a gida domin hana yaduwar cutar Covid19 da ke  barazana a kasashen Duniya.

Gwamna Elrufa’i dai bai fadi lokacin da ake sa ran bude jahar ba, inda mataimakiyarsa ta ce har yanzu ba su gamsu da yanayin da cutar take a jahar ba ballantana su bude jihar.

BBC ta rawaito cewa, daga karshe Malam Nasir El-Rufa’i ya yi wa malamai Allah-ya-isa inda ya ce “ko a Makka ba za a gudanar da  sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau munbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani.
Saboda haka Allah-ya-isa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More