Dakatar da gwamna Rochas na da amfani – Shugaban APC Na Imo

Wasu shugabannin Jam’iyyar APC a Jahar Imo, sun bayyana dakatarwan da aka yi wa gwamna Rochas Okorocha na jahar Imo daga Jam’iyyar ta APC wanda kwamitin gudanarwan Jam’iyyar na kasa ya yi da cewa, hakan ya yi daidai.

Da yake magana da manema labarai a kan hakan a ranar Asabar, wani shugaban jam’iyyar Dakta Jude Agu, cewa ya yi, Okorocha yana yi wa jam’iyyar zagon kasa ne domin nemawa surukinsa nasara ya gaje shi a matsayin gwamnan Jahar.

Agu ya ce, ya kamata a dakatar da Okorocha tun kan  mummunan kullin da yake yi wa jam’iyyar.

Ya ce, kamata ma ya yi kwamitin gudanarwar ya dakatar duk wani wanda yake tare  Okorochan daga cikin jam’iyyar, wadanda a cewar sa duk suna yi wa jam’iyyar zagon kasa ne.

Amma a martanin da Okorocha ya fitar a kan dakatarwan da aka yi masa ta hannun babban Sakataren sa na yada labarai, Mista Sam Onwuemeodo, cewa ya yi wasu shugabannin jam’iyyar ta APC ne suka lashi takobin ganin bayansa a siyasar 2023. Ya kuma ce, an dakatar da shi ne domin a hana ma shi rikan wani babban mukami a Majalisar Dattawa, ya kara da cewa, wannan dakatarwar da aka yi ma shi ba zai yi nasara ba.

Wani Tsohon Kwamishina a Jahar ta Imo, Mista John Anyanwu, cewa ya yi, tun da an dakatar da Okorocha daga Jam’iyyar, akwai alamun samun nasarar Jam’iyyar a zaben gwamna a Jahar.

Ya ce, in har an bar Okorocha, tabbas zai yi kokarin ganin ya kayar da dan takaran jam’iyyar APC a jahar.

Wata shugabar mata ta jam’iyyar ta APC a karamar hukumar Obowo, Rose Ibeawuchi, cewa ta yi, dakatarwan da aka yi wa Okorocha, ta maido da tabbacin da jam’iyyar ke da shi a cikin jahar.

“A yanzun tun da an dakatar da shi, muna da daman shaidawa magoya bayanmu ko wane ne dan takaran jam’iyyar APC a Jihar,” in ji ta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More