Dalilan da suka hana shugaba Buhari halartar wajen muhawara

Shugaba  kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da dalilansa na kin halartar muhawarar ‘yan takaran Shugabancin kasar Najeriya  wanda hukumar shirya muhawarar ‘yan takaran shugabancin kasar  da kafar yada labarai ta kasa (BON), suka shirya.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Barista Festus Keyamo, ya ce, Shugaba Buhari bai halarci muhawarar ne ba saboda ayyukan da ke gabansa da suka hade da lokacin gudanar da muhawarar, da kuma kasantuwar ya halarci wani taro tare da al’umma wanda hakan ya ba shi daman musayar ra’ayi tare da ‘yan Najeriya kai tsaye.

 

“Da farko dai, daga cikin daman da dan takaranmu ya samu na ya gana da ‘yan Najeriya kai tsaye, dan takaran na mu ya yi amfani da wannan daman wajen halartar wani taro na al’umma wanda wata kungiya ta shirya wanda ya gudana a ranar Laraba, 16 ga watan Janairu, 2019. “Tare da shi a wajan tattaunawar akwai Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. ‘Yan Najeriya daga ko’ina da suke a wajen da kuma ta yanar gizo sun yi tambayoyi a kan mahimman batutuwa.

An kuma yada abin kai tsaye a kafafen yada labarai masu yawa na Najeriya,” in ji shi. Festus Keyamo, ya kara da cewa, ayyuka kuma masu yawa na ofis duk suna gaban shugaba Buhari, kuma sun hade da  lokacin gudanar da muhawarar.

Sannan a ranar  Shugaba Buhari ya kaddamar da tashar ruwa ta Baro, a Jahar Neja, ya  kuma je  yakin neman zaben a Jahohin Neja da Filato, inda yawan jama’a ya jinkirta lokacin na shi a duk Jihohin biyu, sai can da yamma ne ya iya komowa Abuja.

Sai  dai muna godiya ga wadanda suka shirya muhawarar a bisa gayyatar da suka yi mana, muna kuma tabbatarwa wa da  ‘yan Najeriya cewa za mu ci gaba da martaba kungiyoyin dake  shirya muhawara irin wannan.

Sannan  yan makwannin da suka shige, Mataimakin dan takaran shugabancin kasar Jam’iyyarmu (APC), Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci Muhawarar da kungiyar ta BON ta shirya,” in ji shi.

A  karshe ya kara  da cewa, maganar da Atiku ya yi babu Buhari a wajen ya nuna cewa shi da Jam’iyyar tasa ta PDP, ba su da wani abin da za su iya tabukawa al’ummar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More