Dalilan da suka sa yan PDP suka ki hallartar taro bada takardar  shaidar su

A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bawa Dakta Abdullahi Umar Ganduje,  mataimakinsa  Nasiru Yusuf Gawuna  tare da kuma ‘yan majalisar jahar takardar shaidar lashe zaben  jahar Kano a zaben da aka gudanar na ranar Asabar 9, da kuma 23 ga watan Maris 2019.

INEC  ta shirya bada takardar shaidar ne ranar Laraba 3 ga watan Afrilu 2019, inda ilahirin masu rawa da tsaki na APC a Jahar Kano  suka hallarci taron tare da masu takewa gwmnan Ganduje baya.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa, yan majalisa 13 da suka yi nasarar lashe kujerar majalisar jahar a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ba su hallarci taron karbar takardar shaidar ta su ba.

Yan majalisar jaha na PDP da sun lashe zaben kananan hukumomin kamar haka:

Dala

Gwale

Fagge

Tarauni

Kibiya

Gezawa

Ungoggo

Bebeji

Rogo

Kumbotso

Nasarawa

Dawakin Kudu
Kano Municipal

 

Hakan yasa OakTVHausa ta tuntubi  shugaban jam’iyyar PDP na jahar Kano,Rabi’u Suleiman idan ya bayyana cewa INEC ta hada kai da gwamnati ne ta hada gagamin taron bikin a filin wasa na Sani Abacha,  domin kowa yasan wajen gwamnati ne, kuma hakan ba shine ka’adar ba da takardar shaidar ba.Shi yasa jam’iyyar su ta PDP ta ki hallartar taron dan gudun yan sara suka.

Rabi’u Suleiman yace bayau suka fara siyasa,  tun 1999 da kuma 2011 sune da gwamnatin har zuwa 2015 suka bada tasu gudumawar Ganduje ya kafa gwamnatin a Jahar Kano, kowa ya gani bahaka akayi ba.

Hakan yasa mukace hukumar zabe tabi ka’ida wajen  bada takardar shaidar lashe zaben na 2019 da ka gudanar.

A karshe Rabi’u Suleiman yace yan jam’iyyar mu sun bi ka’ida kuma sunje sun  karbi takardar shaidar su ta lashe zaben a shedikwatar INEC dake jahar Kano.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More