Dalili da ya hana Buhari rattaba hannu a kan dokar mafi karancin albashi

Fadar shugaban kasa a jiya Laraba sun bayyana dalilan da yasa har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu a kan dokar mafi karancin albashi ba wanda tuni majalisar wakilai da ta dattawa suka sanya hannu suka kuma mikawa shugaban kasar domin tabbatar da shi a matsayin doka.

A ranar 19 ga watan Maris ne, majalisar dattawa suka amince da a biya naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi a kasar ta Najeriya.

Majalisar Dattawa sun bi sahun takwarorinsu ne wato majalisar wakilai bisa amincewa da 30000 a  matsayin mafi karancin albashi.

A makon da ya gabata ne dai, aka yika watsa labarai  a shafukan sada zumunta cewa, shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar albashi mafi karancin. Sai dai a yayin da yake zantawa da Jaridar The PUNCH a Abuja a ranar Laraba 3 ga watam Maris, mai taimakawa shugaban kasar akan harkokin majalisar Dattawa, Sanata Ita Enang, ya yi watsi da wannan rahoton.

Ya ce sanya hannu akan dokar ba a boye za a yi shi ba, domin yadda shugaban kasar ya saba sanarwa da ‘yan kasa matsayarsa akan kowanne abu, haka zai fito ya bayyanawa ‘yan kasa dangane da sanya hannun sa kan dokar.

Enang ya kara da cewa  shugaba Buhari  har yanzu bai sa hannu kan dokar ba, domin har yanzu yana nazarin dokar tare da bin wadansu ka’idoji kafin ya sanya hannu.

Sai dai ya ce tabbas dokar mafi karancin albashin na naira dubu 30 da majalisar kasa suka amince, tuni aka mikawa shugaban kasar.

Ya ce; nan ba da jimawa ba shugaban kasar zai yiwa ‘yan kasa ta Najeriya bayani akan matsayar dangane da dokar.

A karshe Enangya bayyana cewar shugaban kasa ya sanya hannu kan dokar, babu ita a yanzu kuma ba gaskiya bane.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More