Dalilin da ya sa mataimakin gwamnan jahar Ondo fita daga APC ya koma PDP

Mataimakin gwamnan jahar Ondo, Agboola Ajayi ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkar kasar Najeriya, ya koma  babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Hakkan ya faru ne bayan wani dan lokaci kadan  da aka hana  mataimakin gwamnan fita daga gidan gwamnatin jahar wanda ke birnin  Akure, wanda  kwamishinan ‘yan sandan jahar Bolaji Salami da tawagarsa suka yi.

Ana ganin cewa, hakan ne babban dalilin da ya sanya Mista Ajayi ficewa daga jami’iyyar, inda ya bayyana cewa dalilin fitarsa a bayyane yake kowa ya sani.

Jim kadan bayan ficewar tasa Mista Ajayi ya bayyana komawarsa jam’iyyar adawa ta PDP tare da karbar katin shaidarsa na zama dan jam’iyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More