Dalilin da yasa Abdulaziz Yari ya koka da gwamnatin mai ci a Zamfara

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, yayi Allah wadai da irin gallazawa Jigogin  jam’iyyar  APC da ake yi a Zamfara.

Adams Oshiomhole ya koka game da abin da ke faruwa ga‘Ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jahar Zamfara ne, a lokacin da ya gana da wasu jigogin  jam’iyyar na jahar ta Zamfara a ranar Talata 11 ga watan Fabrairu 2020.

Tsohon gwamna Abdulaziz Yari ne yayi jagoranci ‘Ya yan  jama’iyyar APC na jahar zuwa wajen Adams Oshiomhole dan gabatar da korafe-korafen nasu, a shedikwatar APC dake babban birnin tarayyar Abuja.

Sun bayyana  cewa gwamnatin mai ci a yanzu a jahar tasu tana gallaza masu tare da yi musa bazanar rasa ayyuka su indai basu koma jam’iyyar ta PDP ba.

Sai dai Adams Oshiomhole ya bayyana cewa  jam’iyyar APC ta na kokari wajen kawo karshen halin da magoya bayan jam’iyyar su take ciki  tare da yin kira a garesu dasu jajirce a kan matsayar su.

“Kamar yadda ku ke gani yana yiwuwa yau kaine da mulki, gobe kuma ba kai ba ne, dan haka dole doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna wani banbancin siyasa ba.”

Oshiomhole yace yayi mutukar farin ciki da basu sauya sheka zuwa jam’iyyar ta PDP, duba da yadda suka ce ana gallaza masu tare da bankara doka domin cafke mutane kuma a  garkame su ba tare da hakki ba, Dole kowa ya mallaki damar shiga cikin kungiya da damar zuwa inda yake so tare da bada damar mutum ya fadan abin da yake so, wanda bai saba wa dokar damokaradiyyar. (Yancin kai)

“Ni na yi amanna za a iya daure ni, amma ba za ka iya daure kaunar da na ke yi wa jam’iyya ta APC ba, kuma muddin na sa rai a abu to sai inda karfi na ya kare.” Inji Oshiomhole

A karshe ya bayyana farin cikinsa tare yi masu godiya bisa yanda  suka jajirce tare da jurewa wajen ganin an zauna lafiya a jahar, ba tare da sun dauke mataki da kansu ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More