Dalilin da yasa aka hana bukuwan Easter a wasu jahohin

Babban Sufeton ‘yan sanda na Najeriya Muhammed Adamu ya bai wa kwamishinonin ‘yan sanda umarni su ci gaba da tabbatar da dokar hana taruka a jahohin da suke cikin dokar yayin bikin Easter.

A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce Muhammed Adamu ya taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar.

Sufeton ya yi kira ga shugabannin addinai da shugabannin al’umma a jahohin Abuja da Legas da Ogun, inda dokar hana fita ke aiki .

Da su ci gaba da bin dokar sau da kafa sannan su gudanar addu’o’i a gidajensu.

sannan ya roki ‘yan Najeriya da su kalli dokar hana fitar a matsayin daya daga cikin koyarwar Easter da suka hada sadaukarwa, jumuri, hakuri, kauna da kuma nasara, sannan ya jaddada aniyarsu ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More