Dalilin da yasa aka nada Goodluck Jonathan domin sasanta rikicin Mali

Mali tafada cikin rikicin siyasa a makonnin baya bayan nan inda masu zanga-zanga suke kira ga Shugaba Keïta ya sauka daga mulki kan batutuwa da dama ciki har da zaben da ake ce-ce-ku-ce a kansa.

An nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin wakili na musamman da zai sasanta rikicin siyasar kasar Mali.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, Jean-Claude Kassi Brou ne ya sanar da nadin Mr Jonathan.

“Ina amfani da wannan dama, bayan tuntubar shugaban kungiyar nan mai girma Issoufou Mahamadou, shugaban Jamhuriyar Nijar, matsayin da muka dauka na nada ka a matsayin wakili na musamman don magance rikicin Mali,” a cewar wasikar da aka wallafa a jaridun kasar.

Masu zanga-zangar sun samu kwarin gwiwa ne musamman saboda gazawar gwamnati wajen shawo kan rikicin kabilanci da na addini da ke addabar kasar.

Tsohon shugaban Najeriya, Jonathan samu yabo daga kasashen duniya a shekarar 2015 bayan ya amince da shan kaye a zaben da Janar Muhammadu Buhari ya lashe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More