Dalilin da yasa aka yanke wa dan shekara 22 hukuncin kisa a Kano

Wata babbar kotun jahar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

Matashin dan kungiyar Faira ne a darikar Tijjaniya Ya hada wani dandali na Whatsapp da ya yi wa lakabi da Umma Abiha, wato dandalin masoya ‘yar manzon Allah SAW.

A ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu, 2020, a lokacin da suke hirar addini a dandalin aka sami wani ya soki darikar Tijjaniya yana mai zargin suna tafiya dai dai a inda shi kuma ya nadi muryarsa ta (Voice note) inda yayi kalaman batanci ga Manzan Allah SAW, wanda ya yi su ne kan an soki darikar Tijjaniya da yake bi.

A inda bayan yin kalaman nasa ne sai ya siyar da wayar sa ya yi kudin mota zuwa Jigawa don gudun abin da zai je ya dawo.

 Tun a  watan Maris wasu matasa suka yi  zanga-zangar neman a hukunta wani Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci, sun yi cincirundo zuwa gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar  ya tarbe su.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.
An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka.

“A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na 382 (b) na kundin shari’ar Jihar Kano ta shekara ta 2000 ta tanada”.

 Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar daukaka kara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More