Dalilin da yasa Dabazzau bai cikin ministocin da suka yi maimai

Shugaban kasar Najeriya  Muhammadu Buhari, bai sake nada tsohon ministan harkokin cikin gida, Laftanal Janar Abdulrahmana Dambazau (mai ritaya)  a zango mulkin na biyu ba.

Dambazau ya fado cikin tsofin ministoci 18 da shugaba Buhari ya cire sunayensu daga  jerin sunayen mutane 43 da ya sake nadawa ministoci a zangon mulkisa na karo na biyu.

Kamar yadda Jaridar ‘The Whistler’ ta rawaito cewa shugaba Buhari ya ajiye Dambazau ne bayan wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa ya same shi da laifin ‘cin mutuncin aiki’, inda ta ce majiyarta ta bayyana mata cewa Dambazau tsohon shugaban rundunar sojojin Najerriya (COAS) daga 2008 zuwa 2010, ya gaza samun damar koma wa kujerarsa ne bayan an gano cewa yana da hannu wajen badakalar mayar da tsohon shugaban hukumar fansho da ya gudu, Abdulrasheed Maina bakin aiki.

The Whistler ta ce dama shugaba Buhari ne da kansa ya zabi Dambazau domin bashi mukamin minista a wacan karon na farko wato a shekarar 2015.

Sai dai kuma wata majiyar da ta nemi a boye sunanta, ta bayyana cewa Dambazau bashi da goyon bayan shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jahar Kano wato mahaifarsa, a lokacin da shugaba Buhari ya zabe shi domin zama minista a 2015.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More