Dalilin da yasa El-Rufa’i ya tsawaito dokar hana fita na kwaniki 30 a Kaduna

Gwamnatin jahar  Kaduna ta tsawaita dokar hana fita na tsawon kwanki 30  a yunkurinta na dakile yaduwar Coronavirus  a jahar.

Gwamnatin jahar ta sanar a shafinta na Twitter cewa gwanna Malam Nasir Elrufa’i ya tsawaita dokar ne bisa shawarwarin da kwamitin jahar kan cutar Covid19  ta bayar karkashin jagorancin Mataimakiyar gwamnan jahar, dakta Hadiza Balarabe.

Gwamnatin Kaduna kuma ta ce za ta tilasta amfani da abin rufe fuska wato takunkumi, saboda muhimmancinsa wajen rage yaduwar cutar tsakanin mutane da kuma kare lafiyar jama’a.

A ranar 26 ga watan Maris ne gwamnatin Kaduna ta fara sanar da dokar hana fita a jahar, kuma yanzu Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ranar Lahadi 26 ga Afrilu.

Gwamnatin ta umurci jama’a su zauna a gidajensu sannan wuraren ibada da shaguna da wuraren bukukuwa da kasuwanni za su kasance a rufe.

Sanarwar ta ce za a hukunta duk wanda ya saba dokar ta hanyar tara da kuma kwace motarsa.

Sannan gwamnatin Kaduna ta ce yadda cutar ke bazuwa, za ta rufe kofofin shiga jahar, kuma duk wanda aka kama ya shiga ko ya ratsa za a bukaci ya koma inda ya fito ko kuma a killace shi na tsawon mako biyu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More