Dalilin da yasa gwamna Ganduje ya dakatar wani hadiminsa 

Gwamnan Jahar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mai bashi shawara ta musamman kan  harkokin kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai a bisa dalilin sukar shugaba Muhammadu Buhari da yayi a kafar yada labarai.

Kwamshinan yada labarai na jahar Kano, Malam Muhammad  Garbe ne ya isar da umarnin gwamnan cikin wata sanarwa ya fitar a ranar Asabar, inda yace dakatarwa ta fara ikine a ta ke.

Duk da cewa hadimin gwamnan yana da ikon yin tsokaci kan batutuwa bisa ra’ayinsa,amma  a matsayinsa na wanda ke rike da mukami na gwamnati, abune mai wuya ya bambance ra’ayin kankin kanka sa dana matsayin gwamnatin kan al’amuran da suka shafi al’umma. Kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sannan kuma  gwamnan  ya gargadi masu rike da mukamai na siyasa da ma’aikatan gwamnati dasu kiyayye yin maganganu da ka iya tada tarzoma ko janyo wani dumamar siyasa cikin al’umma.

#OakTV #OakTVHausa
#OakTVOnline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More