Dalilin da yasa Gwamnonin Najeriya amincewa da rufe iyakoki 36 na kasar

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince da rufe iyakokin jahohin 36 don hana zirga-zirga a tsakanin jahohin na mako biyu, a wani mataki na dakile yaduwar Coronavirus a kasar.

Najeriya dai na da mutune 981 da ke dauke da cutar Covid19 inda aka sallami mutane 197, yayin da mutane 31 suka mutu.

A wata ganawa da sukayi  ta kafar intanet, gwamnonin sun nemi gwamnatin tarayya da ta sakar musu al’amarin yaki da annobar Covid-19.

Gwamnonin dai da ra’ayin cewa barin iyakokin jahohi ne ke kara ta’azzara yaduwar cutar a kasar.

Yanzu dai abin da ya rage shi ne ko Shugaba Buhari zai sa dokar kulle a jahohin kasar baki daya , ba iya jahohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More