Dalilin da yasa hukamar alhazai ta bukaci su bada kudin ajiya

Hukumar alhazan Najeriya ta bukaci masu niyyar aikin hajjin shekarar 2020 da su ba da kudin ajiya kimanin Naira miliyan daya da rabi 1.5, a kashi uku ga hukumomin alhazansu na jahohi.

Karshe watan da ya gabata ne hukumar ta bawa kamfanonin jirgin yawo da su yi rijistar gudanar da aikin hajji mai zuwa don kauce wa rasa damar tasu.

Sanarwa fito ne daga jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara, wadda ta bayyana a taron masu ruwa da tsaki na komawa sabon ofishin dindindin na hukumar da a ka lakabawa suna “GIDAN HAJJI”.

Hukumar alhazan ta ce, shirin hajjin ya hada da yin rajista a kan lokaci, da biyan kudi kai tsaye na masauki ga masu gidaje don samun rangwame.

Voa ta rawaito cewa,Shugaban hukumar alhazan Barista Abdullahi Mukhtar Muhammed ya ce, cikin sabbin matakai akwai kaucewa cunkoson alhazan musamman a tantunan MUNA da hakan kan faru saboda rashin biyan kudi kan kari.

NAHCON ta ba da dama ga hukumomin alhazan jahohi su rika gudanar da lamuran UMRAH don fadada hanyar su ta kudin shiga, amma da sanya idon hukumar alhazan ta kasa don biyawa masu ibada hakkin su bisa irin kudin da su ka biya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More