Dalilin da yasa kotu tayi fatali da karar masu nadin sarki a Kano

Wata babbar kotu a Kano tayi watsi da karar da masu nadin Sarki a jahar suka shigar domin kalubalantar gwamnatin jahar kan kirkiro sabbin masarautu guda 4 da tayi a shekarar 2019 da ta gabata, wanda sune:Gaya, Rano, Bichi da  kuma Karaye.

Hakan yasa aka samu masarautu guda 5 a  jahar ta Kano, gami data kwaryar birnin Kano, wacce Sarki Muhammadu Sanusi II yake jagoranta.

Sai dai lamarin  bai yi wa masu nada sarki a Kano dadi ba, abin da ya sa suka shigar da gwamnati kara a kotu.

A wajen yanke hukuncin na ranar Litinin ne, alkali Ahmad Badamasi na babbar kotun ya ce abubuwa da dama sun sha gaban karar yayin da hukuncin da alkali Usman Na’abba ya yanke ranar 21 ga watan Nuwamba ya soke dokar da ta kirkiri sabbin masarautun.

Masu nadin sarkin hudu da suka shigar da karar su ne Hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani (Madakin Kano) da Hakimin Wudil Abdullahi Sarki Ibrahim (Makaman Kano) da Hakimin Gabasawa Bello Abubakar (Sarkin Dawaki Mai Tuta da Hakimin Dambatta Mukhtar Adnan (Sarkin Ban Kano).

Premium Times ta rawaito cewa dukkan masu nadin sarkin hudu sun rasa mukaminsu na Hakimi sannan an nada wadanda za su maye gurbinsu.

Wadanda ake kara su ne gwamnatin Kano da gwamnan jahar da shugaban majalisar dokokin Kano da majalisar dokokin jahar da alkalin alkalai na jahar.

Sannan kuma  akwai sabbin sarakunan Aminu Ado Bayero Sarkin Bichi, Ibrahim Abubakar Sarkin Karaye Tafida Abubakar Sarkin Rano da kuma Ibrahim Abdulkadir Sarkin Gaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More