Dalilin da yasa kungiyar Lauyoyin Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Gwamnan El-Rufa’i

Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai, biyo bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka yi kan gayyatar.

A wani sako da kungiyar Lauyoyin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar janye goron gayyatar da ta turawa gwamnan kuma tuni ta shaida wa gwamnan matakin da ta dauka.

Wani lauya ne mai suna Usani Odum ya kaddamar da takardar koke ta intanet inda ya nemi kungiyar ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More