Dalilin da yasa  kwato dukiyar da aka sata aka kai kasar waje ya zama abu mai wahalar gaske – Magu

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Shugaban Hukumar hana cin hanci da karban rashawa na EFCC wato Mista Ibrahim Magu ya bayana cewar, hukumar ta shi tana fafatawa ne da wata kakkarfar   runduna a kan yakin da cin hanci da karban rashawa da take yi.

Sannan ya kuma bayyana takaicinsa na wahalar da ke cikin dawo da kudaden da aka sace da kuma boye su a kasar waje, duba da cewa rundunonin da suke fuskanta masu karfi ne, saboda  dukiyoyin da suka  sata suka  boye masu yawan gaske ne. Kuma suna da karfin da zasu iya tursasa duk wani kokarin binciken namu.

Magu ya bayana hakan ne a  wajen taro na 3 na ranar yaki da cin hanci da karban rashawa a Afrika, wanda hukumar ta EFCC ta shirya a  babban birnin tarayyar Abuja.

A karshe yace  dawowa da wadannan dukiyoyin da kadarorin cikin kasar Najeriya  ya zama matsala sosai,  Inda yace  hukumar ta kuduri aniyar jagorantar yakin da cin hanci da karban rashawa har sai ta ga abin da ya turewa Buzu nadi.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More