Dalilin da yasa Oscar ta fitar da shirin fim din Lionheart daga gasar fim mafi kyau.

Mai ba da umurnin shirya fina-finai kuma jarumar  Nollywood Genevieve Nnaji ta bayyana  rashin jin dadinta kan fitar da fim dinta Lionheart da Oscar ta yi.

Oscar ya fitar da fim din na barkwanci saboda an yi amfani da harshen turanci sosai a ciki, wanda hakan ya saba wa sharadin shiga gasar fim mafi kyau na kasa da kasa domin an fi so a yi amfani da wani harshe ba turanci ba.

A fim din na Lionheart wanda shi ne na farko daga Najeriya wanda ya kai wannan mataki an yi amfani da harshen turanci ne, mintina 11 kawai aka yi ana harshen Igbo a cikin shirin fim din.

Fim din wanda ya samu yabo ana nuna shi ne kan manhajar Netflix, an shirya kada kuri’ar a zaben sashen fim din kasa da kasa a ranar Laraba kafin aka fitar da shi.

Miss Nnaji ta bayyana  korafin ta na korar fim din a shafinta na Twitter inda ta ce “Fim din na nuna yadda mu ‘yan Najeriya ke yin Magana ne”

Ta kara da cewa “wannan ya hada da turanci, wanda shi ne ke sada sama da harsuna 500 da ake magana da su a kasar. Ba mu muka zabi wadanda suka yi mana mulkin mallaka ba. To dai, wannan fim din da  yawa irinsa an yi su ne a Najeriya.”

An bayyana fitar da fim din daga gasar ga masu kada kuri’ar a ranar Litinin a cewar shafin The Wrap.

Fim din na daga cikin 29 cikin 93 wanda mata suka ba da umurnin shirya shi wanda aka gabatar domin neman cin gasar a shekarar ta 2019.

Babbar daraktar mai ba da umurni Ava DuVernay a shafinta na Twitter inda take tambaya idan fitar da fim din ba nufin “haramtawa” Najeriya har abada sake shiga gasar ta Oscar.

Hashen Turanci dai shi ne harshen da ake amfani da shi a matakin gwamnati a mafiya yawan kasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka a Afirka.

Genevieve Nnaji ta ta bada umarni a shirin fin din mai suna “Lionheart”

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More