Dalilin da yasa Punch tace zata kira mulki Buhari “Mulkin Kama-Karya”

Jaridar ta Punch a dab’inta na ranar Larabar 11 ga watan Disamba mai taken “Buhari’s Lawlessness: Our Stand” ta ce ta yanke shawarar daga yanzu za ta rinka makala wa Shugaba Buhari lakabin soja, na Manjo Janar da kuma bayyana salon mulkinsa a matsayin na “kama-karya”.
Jaridar ta raiwato cewa, ta yanke wannan shawara hakkan saboda lura da irin ‘keta hakkokin dan adam’ da Shugaba Buharin yake yi a kasar ta Najeriya, al’amarin da jaridar ta ce ya sha ban-ban da salon mulkin dimokradiyya.

A wani matakin nuna rashin amincewarmu ga salon mulkin kama-karya da na soja, Punch ( a dukkan shafukanta na jarida da intanet da wasanni da daba’in ranar Asabar da na Lahadi) daga yanzu za ta fara makala wa Buhari tsohon matsayinsa na soja na Manjo Janar wanda yake amfani da shi lokacin mulkin soja a shekarun 1980s.

Sannan kuma za mu rinka bayyana gwamnatinsa da ta danniya, har zuwa lokacin da ya fara mutunta dokokin kasa.”
Punch ta zayyana wasu dalilanta da ta ce su ne suka ba ta damar ayyana gwamnatin Shugaba Buhari da ‘kama-karya’ da rashin mutunta doka da oda kamar haka;

1. Batun “kama dan jaridar nan na SaharaReporters, Omoyele Sowore da jami’an hukumar DSS aka ce sun yi a cikin kotu.

2. Yadda ‘yan jaridu suke fuskantar kalubalen fadin albarkacin bakinsu.

3. Kokarin hana jama’a fadin albarkacin bakinsu a soshiyal midiya.

4. Kamawa da tsare ‘yan kasa fiye da awa 48 da jami’an tsaron kasar ke yi karkashin gwamnatin Buhari.

5. Yadda gwamnatin Buhari ke ci gaba da tsare tsohon mai bai wa shugaban kasa Jonathan shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki da jagoran kungiyar IMN da gwamnati ta haramta, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

6. Irin yadda jami’an SSS suka yi wa alkalai dirar mikiya a gwamnatin Buhari.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More