Dalilin da yasa sarkin Bichi ya kori Hakimai guda 5

Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke wasu hakimai  guda biyar saboda kin yi masa mubayi’a tare da maye gurbin su da wasu.

Hakiman da aka cire sun hada da Bichi, Dawakin Tofa, Dambatta, Minjibir da kuma na Tsanyawa.

Hakkan ya farune ne bayan da majalisar jahar Kano ta sake yin wata doka wadda ta kafa sabbin masarautu guda hudu wadanda kotu ta soke a watan da ya gabata.

Kotun ta sanya ranar Talata domin fara sauraron karar.

Kwanaki kadan bayan kafa dokar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nada Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar inda ya umurce shi da ya kira taron zauren.

Sai har  zuwa yanzu dai Sarkin bai kira taron ba inda masarautar Kano ta sake maka gwamnatin jahar Kotu kan kafa sabbin masarautu a jahar.

  • Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Nabahani, wanda shi ne shugaban masu zaben Sarkin Kano.
  • Sarkin Bai Hakimin Dambatta Alhaji Mukhtar Adnan, daya daga masu zaben Sarkin Kano. Ya zama Hakimin tun 1954, abin da ya sa ya fi kowane Hakimi dadewa a masarsutar Kano, domin kuwa ya shafe shekara 64 yana Hakimci kafin a sauke shi a ranar Asabar din nan.
  • Matawallen Kano Hakimin Minjibir Aliyu Ibrahim Ahmed.
  • Barden Kano Hakimin Bichi Alhaji Idris Bayero, wanda uba yake ga Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.
  • Hakimin Tsanyawa Alhaji Sarki Aminu.

Biyu daga cikin Hakiman da aka cire wato Madaki da Sarkin Bai na cikin mutum hudu da suka shigar da karar gwamnan Kano kan sababbin sarakunan da aka nada gaban kotu.

BBC ta rawaito cewa suna kalubalantar kirkirar sababbin masarautu sannan suka nemi kotu ta hana wadanda aka yi kara sauke su daga mukamansu ko daukar wani mataki da zai taba aikinsu na masu zaben Sarki.

Masarautar Kano na daga cikin wadanda suke da tarihi da shekaru da dama a kasar Hausa.

An yi sarakunan Habe sama da 40 kafin Fulani suka karbi mulki a shekarar 1806 inda Sarki mai ci a yanzu Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne na 14 a jerin, Fulani ke mulki bayan da ya gaji Ado Bayero, a 2014 wanda kuma shi ne mahaifin Sarki Bichi na yanzu, Aminu Ado Bayero.

Gwamna Gaduje ne ya kafa sabbin masarautun guda huda, kuma yace za su kawa ci gaba a jahar ta Kano.

Sai dai wasu sukar yin hakkan  sukeyi tare da kin goyar baya hakan, yayin da suke zargin hakkan na iya ruguza tarihin Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More