Dalilin da yasa shugaba Buhari rushe  kwamitin biciken cin hanci da rashawa

Shugaban  kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya rusa kwamitin binciken tafka almundahana bisa dalilin wani abu mai kama da baiwa kura ajiyar nama.

A kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ke yi na ganin an fuskanci alkibilar yaki da cin hanci da karbar rashawa gadan-gadan, gwamnati na daukar mataki kan zargin da ake wa shugabannin kwamitocin da ke yaki da cin hanci da rashawa.

Kwanaki kadan da suka wuce  Shugaba  Muhammadu Buhari ya bada umarnin rushe kwamitin binciken cin hanci da rashawa da kwato dukiyoyi da kaddarorin gwamnati da aka sata nan take, wanda ke karkashin jagorancin Mista Okoi Obno Obla, wanda ake zargi da cin hanci da rashawa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar da ya karbe ayyukan wannan kwamitin, sannan ya rusa shi, kuma ya tabbatar an kammala duk wasu bincike-bincike da aka fara ba tare da daukar wani  lokaci ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More