
Dalilin da yasa shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir sauka daga kan mulki
Rundunar sojojin kasar Sudan ta bayyana kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, bayan da aka shafe watanni ana zanga-zanga a kasar ta Sudan, kuma rundunar ta bayyana soke kundin tsarin mulkin kasar ta Sudan, sanarwar juyin mulki da rundunar ta bada ne ta kawo karshen wa’adin mulkin na shekaru 30 da al-Bashir din yayi a kan karagar mulkin kasar ta Sudan.
Gwamnatin rikon kwaryan wacce rundunar sojojin za ta jagoranta za ta yi riko na tsawon shekaru biyu, kafin a gudanar da zabe
Sannan kuma za a sanya dokar ta baci na tsawon shekaru uku, hakan yasa aka saki dukkan fursononin siyasa da gwamnatin al-Bashir ta garkame,kuma ana kokarin sakin jagororin da suka jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyyar yiwa al-Bashir juyin mulki a kasar.
Mataimakin shugaban kasar Sudan, Awad Ibn Auf ne ya ya bayyana hakan inda ake sa ran za ta kawo karshen zanga-zangar da aka shafe watanni hudu ana yi a kasar ta Sudan.
Masu zanga-zangar bisa dalilin su tsadar rayuwa a kasar ta Sudan,yayin da suka Allah-wadai da gwamnatin al-Bashir.
Sai dai har suwa wannan lokacin ba a kai ga sanin matakan da rundunar sojojin kasar za su dauka ba, yayin da masu zanga-zangar suka yi zaman dirshan a hedikwatar sojojin kasar tare da rera wakar su na “Mun yi Nasara, Ya fadi warwas”
Inda suke nufin sun samu nasarar korar shugaban kasar ta su wato Omar al-Bashir