Dalilin da yasa sojoji mamaye gidan jaridar Daily Trust

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa dakarunta suka mamaye gidan jaridar Daily Trust a Maduguri, Abuja da kuma Legas ranar Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Sani Usman ya ce sojojin kasar tare da sauran jami’an tsaro sun mamaye ofisoshin kamfanin jaridar don “gayyatar wasu ma’aikatan gidan game da wani labari da aka buga a jaridar ranar Lahadi.”

Sani Usman ya ce “labarin ya kunshi wasu muhimman bayanan sirri na rundunar wanda zai iya yin zagon kasa ga tsaron kasa.”

Mai magana da yawun rundunar dai ya zargi jaridar da bayyana abin da rundunar ke shiryawa dangane da ayyukanta a kan Boko Haram.

Ya kuma ce labarin ya bankado wasu muhimman abubuwa da rundunar ke shirya wa da zai amfani ‘yan Boko Haram.

A ranar Lahadi bayan faruwar al’amarim mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin kasar ta umarci rundunar da ta fita daga ofishin jaridar, kuma su tattauna a tsakaninsu don kawo  maslaha a al’amarin.

 

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More