Dalilin da yasa Yakubu Dogara ya bar PDP ya koma APC

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ya ce bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba da gwamnatin jaharsa ta Bauchi ke yi na cikin manyan dalilan da suka sanya shi barin  jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyarsa ta asali APC.

Ya kuma bayyana damuwa kan rashin biyan ma’aikata albashi a kan lokaci, da kuma rashin gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin wata shida na farko, kamar yadda gwamna Bala Muhammad ya yi alkawarin zai yi..

”Gwamnati ta ciyo bashi na Naira biliyan hudu, daga baya aka gano kudin a asusun wani kamfani mai zaman kansa, duk da cewa an ranto su ne da sunan jahar Bauchi, sannan ana bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba, baya ga ninka kudin da ake yi yadda aka ga dama ba tare da bin ka’idojin doka ba.”

Yakubu Dogara ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa. Turaki Hassan yayin zantawa da BBC, inda ya ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda hankoron samun wata dama a APC.

Dogara ya kuma ce wata matsalar da ya gani a jagorancin gwamnatin PDP ta  Bauchi, ita ce rashin girmama manya, da sarakuna da gwamnan ke yi, sabanin alkawuran da ya yi a baya na cewa zai rika daraja su.

Wadannnan dalilai da kuma karin wasu ne suka sanya Yakubu Dogara yaga cewa ba zai iya ci gaba da zama a inuwa daya da gwamna Bala Muhammad ba, in ji Turaki Hassan, mai magana da yawun dogara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More