Dalilin da yasa yasanda suka garkame ASD Sakamokom aurer da yarsa

An cigaba da tsare shahararren attajirin nan na Kaduna tsohon shugaban kafanin motucin fijo (Peugeot Automobile Nigeria) wato Alhaji Sani Dauda, wanda a ka fi kira da ASD, da kuma wasu mutane biyu, bisa zargin bayar da auren yarsa.

Rahotonnin  sun nuna cewa an tsare  Sani Dauda tare da mutane 2, Alkalin kotun Shari’a da ke Magajin Gari a karamar hukumar Kaduna ta Arewa Malam Murtala Nasir madaurin auren, da kuma daya daga cikin ya’yan sani, wato  Shehu Dauda sakamakon rashin jin dadin mijin ta na farko.

An daura auren Nasaiba Dauda ne a ranar 9 ga watan Nuwamba 2019.

An garkame mutane ukun ne a ranar Litinin 11 ga wata,inda akayi awun gaba dasu zuwa sashen yan fashi da makami ta hedikwatar yansanda dake jahar Kaduna.

Sai dai manema labarai sunyi kokarin jin ta bakin alkalin wayanda ake tuhuma Sani Katu, inda ya bayyana cewar ana zargin tohon mijin Nasaiba Dauda cikin al’amarin.Yayin da kakakin rundunar ‘yan sandan na Jahar Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya ce ba shi da masaniya a kan abinda ke faruwa, tare da yin alkawarin zai bincikar al’amarin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More