
Dalilin da yasa gwamnatin Amurka ta hana wasu yan siyasar Najeriya biza
Gwamantin Amurka ta bayyana dalilin da yasa a ta hana wasu fitattun ‘yan siyasar Najeriya takardar izinin shiga kasar saboda zargin da take yi musu na keta dokokin zabe.
Gwamnatin ta Amurka ba ta bayyana sunayen ‘yan siyasar ba sai dai ta ce suna cikin mutanen da ke karan-tsaye a harkokin zaben kasar, a sanarwar data fitar.
Hakan na faruwa ne kwanaki kadan kafin gudanar da zaben gwamna a jahohin Edo dakuma Ondo da ke kudancin kasar ta Najeriya, wanda ke cike da zaman dar-dar.
Amurka ta yi zargin cewa ‘yan siyasar na da hannu a rikicin zaben da aka gudanar a jahohin Bayelsa da kuma Kogi a watan Nuwamba na 2019.
Dakta Abubakar Kari na Jami’ar Abuja Masana harkokin siyasa sun ce daukar matakin hakkan, yana da kyau wajen inganta mulkin dimokradiyya.
Hana ‘yan siyasar biza na nufin ba za a bar su su shiga kasar ta Amurka ba.