Dalilin hana tashe a Jahar Kano

Jahar Kano ta kasance ta farko a  jahohin arewacin Najeriya, wajen yanda mutanen cikin suka daukar  tashe da mahimmacin tara nishadantarwa a watan Ramdana, yayin da yakai kwana  10,sun kan fita su shirya barkoncin daban-daban, har ma da fadarkarwa da kuma kade-kade da wake-wake.

Sai dai a jahar Kano wadda take a matsayin daya daga cikin manyan yankuna na kasar Hausa, abin ba haka yake ba.

Domin kuwa kamar yadda ta faru a wasu shekarun baya, a wannan karo ma hukumomi a jahar sun haramta gudanar da wannan al’ada mai dinbin tarihi.

A yanzu haka tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar ta Kano ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka kama ya taka dokar hana yin tashe a jihar.

DSP Haruna Kyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yansanda a jihar ya ce jami’an ‘yan sanda na yin sintiri a cikin dare domin tabbatar da cewa ba a bari masu neman tayar da fitina sun cimma burinsu ba.

Ya ce “ba wai tashen ne laifi ba, a’a. Amma bata gari da suke bin ‘yan tashen suke fakewa da haka suke yin kwace da sauran miyagun laifi shi ne ba ma so.”

Ya kuma kara da cewa rundunar za ta rika sintiri a lungu da sako na jahar daga lokacin sallar magariba zuwa karfe goma na dare don kama masu karya doka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More