Dalilin Jifar Oshiomhole a jahar Ogun

An jefi shugabn jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomhole a yayin da shugaba Muhammadu Buhari yaje yakin nemana zaben sa  a birnin Abeokuta na jahar Ogun a jiya Litinin 11 ga watan fabrairu 2019

Abubuwa sun jagule  a wajen yakin nemen zaben  bayan  shugaban jam’iyyar ya ambaci sunan dan takarar gwamna na jahar karkashin  jam’iyyar ta APC, Mista Dapo Abiodun a lokacin da yake yin jawabi ga jama’ar da ta halarci taron.

Suna jin sunan Mista Abiodun daga bakin shugaban APC sai jama’a suka fara yi wa Mista Oshiomhole ihu har wasu ma suka rika jifansa da abubuwa daban daban a filin wasa na MKO Abiola International Stadium.

Hakan yasa  gwamnan jahar Mista Ibikunle Amosun, wanda ke goyon bayan wani dan takarar na daban da ke jam’iyyar APM ya tashi ya roki mutane su kwantar da hankalinsu saboda kar su kunyata sa a gaban shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda ya ce.

Har sai da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya lallashi jama’a kafin suka natsu a wajen gangamin.

Daga nan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nasa jawabin, amma bayan da ya daga hannun dan takarar jam’iyyar ta APC sai mutane suka sake fusata har suka cigaba da jifar tawagar shugaban.

Lamarin ya kai sai da jam’ian tsaro suka rika kare shugaban kasar daga masu jifa kafin a gama taron.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More