Dalilin tafiyar shugaba Buhari Kasar Tokyo

Lahadi 26 ga watan Agusta 2019 Shugaba Buhari na Najeriya yayi tafiya zuwa kasar Japan, a karo na farko bayan kaddamar da sabuwar majalisar zartarwa.
Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina , ya ce shugaban zai halarci wani taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afirka karo na bakwai, da ake yi wa take da TICAD7 da za a gudanar a birnin naTokyo.

Shugaba Buhari zai gabatar da mukala a lokacin taron, a inda zai fayyace alakar Najeriya da Japan da kuma darussan da Najeriyar za ta dauka daga taron da aka yi karo na 6 a Kenya mai taken TICAD6.

Shugaba Buhari zai halarci wani zaman cin abinci da gwamnatin kasar ta shirya sannan kuma zai amsa gayyatar Sarki Naruhito domin zuwa fadarsa ta Imperial Palace, da ke birnin Tokyo domin shan shayi tare.
Bugu da kari shugaba Buhari zai gana da firaiminista Shinzo Abe, da kuma saduwa da wasu manyan shugabannin kamfanonin kasar Japan da suka zuba jari a Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari zai koma Gida Najeriya ranar Asabar 31 ga watan Agusta 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More