Dalilin tsige tshon mataimakin gwamnan Jahar Kogi

Majalisar jahar Kogi ta bayyana cewar, bakin alkalami ya raga ya bushe. Yayin ta yi karin haske kan tsige tsohin mataimakin Gwamnan Jahar Kagi wato Simon Achuba.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Kogi, Honarabul Moses Akande ya zargi kwamitin da aka kafa na musamman domin ya binciki tsohon mataimakin gwamnan jahar da yin ba daidai ba a aikinsu. Dan majalisar mai wakiltar shiyyar Ogorimangogo a jam’iyyar APC da yake magana a madadin daukacin majalisar dokokin jahar yace ba a sa wannan kwamiti ta fitar da wata matsaya ba, illa ta yi bincike. Kwamitin da aka kafa sun yi aikinsu, sun gabatar mana, mu kuma mu ka dauki mataki.
Tsarin aikin shi ne kwamiti za ta yi bincike ne, daukar hukunci ba na ta bane.Kuma haka su ka amince wajen aikin.
 
Daukar matakin cewa mataimakin gwamna ya na da gaskiya ko bai da gaskiya aikin majalisar dokoki ne. Ita kadai ta ke da hurumin bayyana wani aiki ne ya zama ba daidai ba.” Inji Honarabul Akande.
 
Majalisar tace sashe na 188(11) na kundin tsarin mulki ya ba ta wannan dama.
 
Akande yake cewa bai san daga inda rahoton kwamitin yake yawo ba bayan da farko shugaban kwamitin ya kira aikin da sirri. Akwai alamar tambaya a game da jawabin da ake cewa shugaban kwamitin, Barista John Baiyeshea, ya yi. Idan kwamitin sun mikawa wani daban rahotonsu, ya nuna cewa sun yi wasa da aikin na su.
 
Kowa ya san yadda mataimakin gwamnan da aka tsige ya tafi gaban talabijin ya na maganar wasu bayanan sirri, wanda ya sabawa rantsuwar da ya yi, wannan ba babban laifi bane,Akande ya tambaya, majalisar tace Achuba ya yi karya da yace ba a biyansa albashinsa domin hujjoji sun nuna ana biyansa. Aikin kwamiti mu ka yi amfani da shi wajen daukar mataki. Idan bai amince da haka ba, ya tafi kotu.
 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More