Dalilin yasa na zabga wa Akpabio mari – Joy Nunieh

 Tsohuwar shugabar  hukumar raya yankin  Niger Delta  Delta wato NDDC, Joy Nunieh ta bayyana cewar, ta zabga wa ministan kula da harkokin  Neja Delta, Godswill Akpabio, tsohon , mari sakamakon ya  nemi yayi lalata da ita.

Nunieh ta bayyana hakkan ne a lokacin da take hira  da gidan talabijin na Arise, inda tace lamarin  ya faru ne a gidan da  ministan yake saukar bakin da ke birnin Abuja.

Ta ce martanin da tayi masa yayin da ya nemi yin lalata da ita na nuna cewa bata daukar wulakanci a matsayinta na ‘yar asalin jihar Ribas.

“Me yasa bai sanar da cewa na maresa ba a gidan saukar bakin sa da ke Apo? Ni ce mace daya da ta taba marin Akpabio. Ya yi kokarin yin lalata dani.” Inji ta.

Ta kara da cewa, “Na zabga mishi mari. Daga Ogoni nake kuma ba a wasan banza da mu. Na nunawa Akpabio cewa matan jahar Ribas basu daukar wulakanci.”

Tsohuwar shugaban NDDC ta zargi Akpabio da kara kudin kasafin hukumar.

Ta ce ministan ya umarceta da saka wasu ayyuka na hukumar ‘yan gudun hijira a cikin kasafin kudin NDDC.

“Akpabio ya rubuta min jerin wasu ayyuka na hukumar ‘yan gudun hijira don sakawa a kasafin kudin NDDC,” tace.

Nunieh da Akpabio suna ta jifan junansu da zargi daban-daban bayan bayyana bincikarsu da ake a kan wasu kudin hukumar har N40 biliyan.

Ta zargi cewa, Akpabio ya bukaceta da ta canja dalolin da ke asusun bankin NDDC zuwa Naira, ta kori shugaban tawagar lauyoyin hukumar wanda dan arewa ne,tare da cewa ta cire dukkan daraktocin da suka ki bin umarninsa tare da yi wa Peter Nwaoboshi sharri.

Kamar yadda Nunieh tace, Akpabio ya ja mata kunne da cewa idan bata aikata abinda yake so ba zai tsigeta.

Ta kara zargin Akpabio da cewa, baya taba sa hannunsa a kan wata takarda sai dai ya sa mukarrabansa su yi damfara.

Ta ce ministan ya bukaceta da ta yi rantsuwar sirri don ya hanata fallasa shi amma ta ki.

“A ranar farko da muka hadu muna hanyar tafiya rantsarwa, ya ce min idan har ban yi abinda yake so ba, zai koreni ba tare da jinkiri ba.” A cewar Nunieh.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More