Dalilin yasa ‘yan sanda suka kama shugaban wadanda suka yi zanga-zanga a jahar Katsina

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya,Coalition of Northern Groups (CNG), ta ce rundunar ‘yan sandan kasar ta kama Nastura Ashir Sharif, shugaban kwamitin amintattunta saboda zargin ya zagi Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin, Abdul-Azeez Suleiman, ya shaida wa BBC ranar Laraba cewa an kama Ashir Sharif bayan sun kammala zanga-zanga a birnin Katsina inda suka yi kira a ɗauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Ya ce an tafi da shi hedikwatar rundunar da ke Abuja, babban birnin kasar inda yake tsare yanzu haka.

Sanarwar da suka fitar tun da fari ta ce “kungiyar CNG ta yi matuƙar kaɗuwa ganin cewa gwamnatin da ke ikirarin kare mulkin dimokradiyya za ta iya hantarar mutanen da suka fito don kare nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu”. Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da  suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe- kashe a yankin.

Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jahohi 19 da ke arewacin ƙasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More