Dalilin zuwan Buhari kasar Afrika ta Kudu

A ranar Laraba 2 ga watan Oktoba 2019 ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar kwanaki uku zuwa kasar Afrika ta Kudu domin tattauna wa a kan walwalar ‘yan Najeriya mazauna kasar.

Gwamnoni 3, ministoci 7 da wasu hadimai 3 ne zasu raka shugaban Buhari zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne bisa bukatar shugaban kasar Afrika ta Kudu wato Cyril Ramaphosa, domin tattauna wa a kan hare-haren da aka dinga kai wa bakin haure, musamman yan Najeriya na kasar.

Buhari yayi balaguron ne tare da gwamnan jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jahar Ebonyi Dave Umahi da kuma gwamnan jahar Filato Simon Lalong.

Ministoci bakwai da zasu raka Buhari sune:

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeam, ministan tsaro Bashir Salihi Magashi, ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, ministan tama da karafaOlamilekan Adegbite, ministan harkokin ‘yan sanda Maigari Dingyadi , karamar ministar saka hannun jari da masana’antu Maryam Katagum da kuma ministan lantarki Saleh Mamman.

Garba Shehu ya bayyana cewa , shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afrika ta kudu bisa gayyatar da shugaban kasar Cyril Ramaphosa, yayi masa domin tattauna walwalar yan Najeriya mazauna kasar da kuma kulla sabuwar alaka a tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari zai gana da yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu, domin jin halin da suke ciki tare da basu tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta cigaba da aiki da gwamnatin kasar Afrika domin tabbatar da kare lafiyarsu tare dukiyoyinsu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More