Dattawan Arewa sun maganatu kan martani Buhari bisa rikicin Ganduje da Sanusi

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi watsi da ikirarin shugaban kasar da ke cewa ba shi da ikon shiga tsakanin a rikicin masarautar Kano.

Hakkan na nufin  tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da  Sarki Muhammadu Sanusi II saboda tsarin mulkin Najeriya ya yi masa iyaka.

BBC ta rawaito cewa Kungiyar ta ce a matsayin shugaban kasar mai jagoran al’umma, ba daidai ba ne ya tsame kansa ya koma gefe lokacin da wani abu da ka iya barazana ga zaman lafiya da tsaron wani sashen kasar ya kunno kai,yin hakan ba zai zama hawan kawara ga tsarin mulkin kasa ba, cewar kungiyar.

Sai dai a martanin da shugaba Buhari ya mayar  ta hanyar mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya ce shugaban a matsayinsa  na wanda aka zaba kan tafarkin dimokuradiyya ya san huruminsa.

Idan lamari yana gaban kotu ko majalisa, shugaba Buhari ba shi da hurumin sa baki, domin idan ya sa baki ya karya doka.”

“Yana ganin gwamnatin Kano ce za ta magance duk wata matsala da ta taso da ke cikin huruminta,” in ji Garba Shehu.

Amma dattawan na arewa na ganin akwai abubuwa da dama da shugaba zai yi ba sai kundin mulki ya ce ya yi wanda ba zai sa ya karya kundin tsarin mulkin ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More